Yanda 'Ƴan Daba Su ka Cinna Wa Wata Unguwa Wuta Cikin Dare a Kano
Al'ummar unguwar Rijiya Biyu a ƙaramar hukumar Dala ta jihar Kano sun kwana cikin tsoro da damuwa bayan wasu ƴan daba sun cinna wuta a wurin sayar da karan yin gurasa da ke yankin.
Rahotanni da suka iso hannun jaridar ZANCEN YAU247 daga wajen lamarin sun bayyana cewa tarin ƴan daba ne suka isa unguwar ɗauke da makamai, inda suka cinna wuta a wajen karan sannan suka yi wa mutane barazana.
Jaridar ZANCEN YAU247 ta samu hotuna da bidiyo da mazauna unguwar suka rinka yadawa a daren wadanda su ka nuna yadda wutar ta yi zafi sosai, abin da ya sa mazauna unguwar neman taimako da gaggawa.
Wasu 'yan ungiwar sun shaida wa jaridar ZANCEN YAU247 cewa wannan lamari ya jawo tsoro a cikin al'umma, inda suka yi kira ga hukumomin tsaro da su dauki mataki cikin hanzari domin kare rayuka da dukiyoyin jama'a.
Comments
Post a Comment