Amarya Ta Hallaka Angonta Kwanaki Bayan Aure a Jigawa

Al’umma a ƙauyen Gauza, ƙaramar hukumar Jahun a Jihar Jigawa sun shiga ruɗani bayan bayyanar labarin cewa wata sabuwar amarya ta hallaka mijinta kwanaki kaɗan bayan an ɗaura aurensu.

A cewar bayanan da rundunar ‘yan sandan Jihar Jigawa ta fitar, lamarin ya faru ne a ranar 23 ga Janairu, 2026. Rahotanni sun nuna cewa mijin ya fara jin matsanancin rashin lafiya ne bayan ya ci abincin da matarsa ta dafa masa. Daga bisani aka garzaya da shi asibiti, inda ya rasu.

Bayan faruwar lamarin, ‘yan sanda sun kama matar marigayin domin gudanar da bincike. A yayin tambayoyi, ana zargin matar ta amsa cewa ta sanya maganin bera (guba) a cikin abincin mijinta da gangan. Ta kuma bayyana cewa ba ta son auren tun farko, tana mai cewa iyayenta ne suka tilasta mata yin sa.

Rundunar ‘yan sandan ta ce ta fara cikakken bincike kan lamarin, kuma da zarar an kammala shi, za a gurfanar da wadda ake zargin a gaban kotu domin ta fuskanci hukunci bisa doka.

Lamarin ya janyo ce-ce-ku-ce a kafafen sada zumunta, inda jama’a da dama ke nuna alhini da kuma damuwa kan matsalar tilasta aure, wadda har yanzu ke ci gaba da jawo rikice-rikice da asarar rayuka a wasu sassan ƙasar nan.

Masana zamantakewa da jaridar ZANCEN YAU24 ta zanta da su, sun yi kira ga iyaye da shugabannin al’umma da su daina tilasta aure, tare da ƙarfafa tattaunawa da fahimtar juna a tsakanin ma’aurata domin kauce wa irin wannan mummunan lamari.

Comments

Popular posts from this blog

BREAKING: FG Approves 40% Pay Rise —Non-Academic Staff Left Out

Nigeria’s Ivory Towers in Ruins: An Investigative Look at the Dilapidated State of Nigerian Universities

BREAKING: US Finally Withdraws from WHO