‘Yan Bindiga Sun Ba Al’ummomin Kankia Wa’adin Kwana 6 — Sun Nemi Shanun 700 da Tumaki 1,000 Ko Su Kai Hari


Mazauna wasu ƙauyuka a ƙaramar hukumar Kankia ta Jihar Katsina sun shiga firgici bayan wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun aike musu da wasiƙa suna ba su wa’adin kwanaki shida su bayar da shanun 700 da tumaki 1,000, in ba haka ba za su kai hari.

Rahotanni sun nuna cewa an kai wasiƙar barazanar ga al’ummomin da abin ya shafa a ranar 6 ga Afrilu, inda aka ba su wa’adi har zuwa Jumma’a, 10 ga Afrilu, su cika wannan buƙata.

An ce ‘yan bindigar sun gabatar da wannan buƙata kamar wani nau’in haraji da suke tilasta wa mazauna yankin biya domin kauce wa hare-hare.

Daga cikin ƙauyukan da aka ambata sun haɗa da, Sukuntuni, da Unguwar Tsamiya, da Magama, da Walawa, da kuma Tudun Wulli

Rahotanni sun ce an ga ‘yan bindiga suna yawo a kan babura a yankunan, abin da ya ƙara jefa jama’a cikin tsoro.

An ruwaito cewa mazauna da dama sun fara gudun hijira daga gidajensu saboda tsananin tsoro; a yayin da iyalai da dama sun koma garuruwan kusa domin neman tsaro

Mahukuntan tsaro da gwamnatin Jihar Katsina sun buƙaci jama’a su kwantar da hankalinsu, suna masu cewa ana ci gaba da ɗaukar matakan tsaro domin kare rayuka da dukiyoyi.

Sai dai duk da wannan kira, har yanzu fargaba na ci gaba da ƙaruwa a yankunan da abin ya shafa.

Comments

Popular posts from this blog

BREAKING: FG Approves 40% Pay Rise —Non-Academic Staff Left Out

Nigeria’s Ivory Towers in Ruins: An Investigative Look at the Dilapidated State of Nigerian Universities

BREAKING: US Finally Withdraws from WHO