Ɗan Majalisar Wakilai, Muhammad Hassan Ya Rasu Yana Da Shekaru 66


Ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar mazaɓar Dawakin Kudu/Warawa a Jihar Kano, Muhammad Danjuma Hassan, ya rasu yana da shekaru 66 bayan fama da jinya.

Rahotanni sun ce marigayin ya rasu ne a ranar Juma’a, 10 ga Afrilu, 2026, a birnin Abuja, bayan wani lokaci yana jinya.

An zaɓi marigayin a shekarar 2023 ƙarƙashin jam’iyyar (NNPP), a matsayin ɗan majalisar wakilai.

Shugaban Majalisar Wakilai, Abbas Tajudeen, ya bayyana rasuwar tasa a matsayin babban rashi ga majalisa, iyalansa da al’ummar mazaɓarsa, tare da miƙa ta’aziyya ga iyalansa da gwamnatin jihar Kano.

Comments

Popular posts from this blog

BREAKING: FG Approves 40% Pay Rise —Non-Academic Staff Left Out

Nigeria’s Ivory Towers in Ruins: An Investigative Look at the Dilapidated State of Nigerian Universities

BREAKING: US Finally Withdraws from WHO