Sojojin Najeriya Sun Yi Ƙarin Haske Kan Yadda Janar Braimah Ya Rasa Ransa
Rundunar Sojin Najeriya ta yi ƙarin haske kan yadda Oseni Braimah ya rasu, inda ta tabbatar da cewa an kashe shi ne yayin wani harin ta’addanci da aka kai wa sansanin sojoji a Jihar Borno State.
Sojojin sun ce marigayin Janar ya rasu ne a lokacin da yake jagorantar dakarunsa wajen mayar da martani ga harin ‘yan ta’adda, kuma ba gaskiya ba ne rahotannin da ke cewa motarsa ta lalace kafin mutuwarsa.
Haka kuma rundunar ta bayyana cewa jami’ai huɗu kacal ne suka rasa rayukansu a harin, saɓanin jita-jitar da ke yawo cewa an kashe sojoji da dama.
Comments
Post a Comment