Rikici Ya Ƙara Tsananta A Jam’iyyar ADC, Magoya Bayan Nafiu Bala Sun Yi Zanga-Zanga A Abuja
Magoya bayan wani ɓangare na jam’iyyar (ADC) ƙarƙashin jagorancin shugaban ɓangaren jam’iyyar na ƙasa, Mafiya Bala, sun gudanar da zanga-zanga a birnin a Tarayyar Nigeria ranar Alhamis.
Masu zanga-zangar sun nuna adawa da abin da suka kira katsalandan da wasu manyan ‘yan siyasa ke yi a harkokin cikin gida na jam’iyyar.
Ana kallon wannan rikici a matsayin wani babban ƙalubale ga jam’iyyar ADC yayin da ake tunkarar zaɓen shekarar 2027, domin rikicin na iya shafar haɗin kan ‘yan adawa da kuma shirinsu na zaɓe.
Comments
Post a Comment