Masu Garkuwa Sun Bai Wa Gwamnatin Tarayya Wa’adin Kisa Kan Mutane 176 da Suka Sace

Masu garkuwa da mutane da ake zargin ‘yan ta’addan Boko Haram ne sun bai wa Gwamnatin Tarayya wa’adin kwanaki guda domin biyan kuɗin fansa kan mutane 176, mafi yawansu mata da yara, da aka sace a ƙaramar hukumar Kaiama da ke jihar Kwara.

Rahotanni sun ce masu garkuwar sun nemi a biya Naira miliyan 20 kan kowane mutum, tare da yin barazanar kashe wasu daga cikin waɗanda suke tsare da su idan ba a biya kuɗin fansar cikin wa’adin da suka bayar ba.

Al’ummar yankin da iyalan wadanda abin ya shafa na kira ga hukumomin tsaro da su gaggauta ɗaukar mataki domin ceto rayukan mutanen da aka sace.

Comments

Popular posts from this blog

BREAKING: FG Approves 40% Pay Rise —Non-Academic Staff Left Out

Nigeria’s Ivory Towers in Ruins: An Investigative Look at the Dilapidated State of Nigerian Universities

BREAKING: US Finally Withdraws from WHO