🛑Gwamna Zulum Ya Goyi Bayan Harin Sojoji, Ya Ce An Rufe Kasuwar Jilli Shekaru 5 Da Suka Shuɗe


Maiduguri, Jihar Borno — Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya bayyana cikakken goyon bayansa ga rundunar sojin saman Najeriya bayan harin sama da ta kai a kasuwar Jilli, yana mai cewa kasuwar an rufe take tun kusan shekaru biyar da suka gabata.

Rahotanni sun nuna cewa jirgin yaƙi na sojin saman Najeriya ya kai hari a yankin Jilli, kusa da iyakar jihar Barno da Yobe, a yammacin ranar Asabar.

An ce harin ya nufi wasu da ake zargin ‘yan ta’adda ne da suke amfani da wurin a matsayin sansani ko cibiyar gudanar da harkokinsu. Sai dai rahotanni sun tabbatar da cewa wasu fararen hula sun rasa rayukansu yayin da wasu da dama suka jikkata.

A wata sanarwa da ya fitar, Gwamna Zulum ya ce:
Gwamnatin jihar ta rufe kasuwar Jilli tun shekaru biyar da suka wuce saboda matsalar tsaro.

Bayan rufe kasuwar, wurin ya koma mafaka ga ‘yan ta’adda da masu kai musu kayan aiki.

Ya jaddada cewa gwamnatinsa na aiki kafaÉ—a da kafaÉ—a da jami’an tsaro kafin a sake buÉ—e kowace kasuwa ko gari a yankunan da rikici ya shafa.

Ana ci gaba da tantance adadin mutanen da suka mutu da kuma waÉ—anda suka jikkata.

Comments

Popular posts from this blog

BREAKING: FG Approves 40% Pay Rise —Non-Academic Staff Left Out

Nigeria’s Ivory Towers in Ruins: An Investigative Look at the Dilapidated State of Nigerian Universities

BREAKING: US Finally Withdraws from WHO