Ƙarfafa Noma: NAERLS Ta Jaddada Goyon Baya Ga Kungiyoyin Manoma Mata a Zariya


Ma'aikatar bincike, da wayar da kan manoma da kuma yaɗa dabarun noma ta ƙasa wato (NAERLS) ta jami’ar Ahmadu Bello University da ke Zariya, ta sake jaddada ƙudurinta na tallafa wa ƙungiyoyin manoma domin su ƙara yawan amfanin gona tare da dogaro da kansu a harkokin noma.

Babban Daraktan cibiyar, Farfesa Yusufu Sani Ahmed, ne ya bayyana hakan yayin bikin cika shekara uku na ƙungiyar Anguwan Alƙali Multipurpose Cooperative Society tsagin mata, da aka gudanar a harabar cibiyar da ke Samaru, a cikin birnin Zaria.

A jawabin da ya gabatar ta bakin mataimakinsa, Farfesa Jamilu, ya bayyana cewa cibiyar na aiki kafaɗa da kafaɗa da ƙungiyoyin haɗin gwiwa ta hanyar ba su horo da sake horaswa kan yadda za su inganta harkokin noma ta amfani da ingantattun iri da sabbin dabarun zamani.

Ya kuma jaddada cewa NAERLS za ta ci gaba da tallafa wa manoma mata domin su samu ƙarfin gwiwa, su tsaya da kafafunsu, tare da zama masu cin gashin kansu a fannin noma.

A nasa jawabin, Sarkin Zazzau, Mai Martaba Ahmad Nuhu Bamalli, wanda Madakin Gonan Zazzau, Alhaji Ibrahim Musa Bamalli, ya wakilta, ya yaba da ƙoƙarin ƙungiyar mata ta Anguwan Alkali bisa hangen nesan da take da shi na zama mai dogaro da kanta ta hanyar noma.

Tun da farko, shugabar ƙungiyar, Malama Hauwa’u Ahmad, ta gode wa Allah da ya ba su damar ganin wannan rana ta cika shekara uku da kafuwar ƙungiyar, tare da yaba wa baƙi da suka halarci bikin. Ta bayyana tafiyar kungiyar a matsayin nasara mai ma’ana.

Comments

Popular posts from this blog

BREAKING: FG Approves 40% Pay Rise —Non-Academic Staff Left Out

Nigeria’s Ivory Towers in Ruins: An Investigative Look at the Dilapidated State of Nigerian Universities

BREAKING: US Finally Withdraws from WHO