ƳAN SANDAN NAJERIYA SUN BUƊE BABBAN OFISHIN PDP NA ABUJA
'Ƴan sandan Najeriya sun buɗe hedikwatar jam’iyyar PDP ta ƙasa da ke Wuse Zone 5, Abuja, bayan shafe lokaci yana a rufe, biyo bayan taƙaddama da tashin hankali a cikin jam’iyyar.
Rahotanni sun nuna cewa an rufe ofishin ne sakamakon rikicin cikin gida tsakanin ɓangarorin PDP masu hamayya da juna, wanda ya kai ga rikici da kuma fargabar taɓarɓarewar tsaro.
An ce rikicin ya samo asali ne daga rigimar shugabanci da kuma zargin wasu ɓangarori na jam’iyyar kan sahihancin shugabanci bayan taron jam’iyya, lamarin da ya haddasa fargaba a hedikwatar.
A lokacin rikicin, jami’an tsaro sun yi amfani da barkonon tsohuwa domin tarwatsa magoya baya, tare da kulle ginin domin hana ƙarin tashin hankali.
Sai dai a yanzu, bayan da aka samu sauƙin rikicin, ƴan sanda sun buɗe hedikwatar wanda hakan ya ba da damar komawar ma’aikata da ci gaba da harkokin gudanarwa.
Comments
Post a Comment