AN JI EL-RUFAI YANA TAMBAYA: “GOBE NE TARONMU, KO?” Yayin da Ya Isa Kotu Kan Shari’arsa a Kaduna


Tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir Ahmad El-Rufai, ya isa Babbar Kotun Jihar Kaduna a ranar Litinin domin ci gaba da shari’ar da ake yi da shi, inda aka ji yana tambaya game da babban taron jam’iyyar sa ta (ADC).

A wani bidiyo da ya karaɗe kafafen sada zumunta, an ji El-Rufai yana tambaya cikin natsuwa yayin da yake cikin harabar kotu:
“Gobe ne taronmu, ko?” — tambayar da ta jawo hankalin jama’a, tare da nuna yadda yake ci gaba da bibiyar harkokin siyasa duk da shari’ar da yake fuskanta.

Rahotanni sun nuna cewa El-Rufai ya isa kotun ne tare da tawagar lauyoyinsa.

Ana dai zargin Nasir Elrufa'i da wasu laifuffuka da suka shafi harkokin mulki, zarge-zargen da ya sha nanatawa cewa ba su da tushe, kuma ya musanta su baki ɗaya.

Majiyoyin jaridar Zancen Yau247 sun tabbatar cewa kotu ta ɗage zaman shari’ar zuwa wani lokaci na gaba domin ci gaba da sauraron ƙarar, yayin da ake sa ran za a yanke hukunci kan wasu buƙatu da ɓangarorin shari’ar suka gabatar.

Comments

Popular posts from this blog

BREAKING: FG Approves 40% Pay Rise —Non-Academic Staff Left Out

Nigeria’s Ivory Towers in Ruins: An Investigative Look at the Dilapidated State of Nigerian Universities

BREAKING: US Finally Withdraws from WHO