Zanga-zangar Adawa Da Manufofin Trump Ta Karaɗe Jihohin Amurka Da Wasu Ƙasashen Duniya

Dubban daruruwan mutane sun fito kan tituna a sassa daban-daban na Amurka da wasu ƙasashe na duniya domin gudanar da zanga-zangar da aka yi wa laƙabi da “No Kings”, wadda ke nuna adawa da manufofin gwamnatin Shugaban Amurka, Donald Trump.

Rahotanni sun bayyana cewa an shirya dubban gangami fiye da 3,000 a dukkan jihohin Amurka guda 50, inda masu zanga-zangar suka taru a manyan birane kamar New York, Washington DC da Los Angeles. Haka kuma, an ce gangamin ya bazu zuwa aƙalla kasashe 15 a duniya, inda aka gudanar da irin waɗannan taruka a wasu manyan biranen Turai da Asiya.

Masu shirya zanga-zangar sun bayyana cewa sun fito ne domin nuna damuwa kan salon shugabanci na Shugaba Trump, da kuma tsoron kar yaƙin da Amurka ke yi, wanda ƙasashe da dama ke tsoron zai iya rikiɗewa zuwa babban rikici a duniya.

Masu zanga-zangar na ɗauke da alluna da ke da saƙonni kamar “No Kings”, “Kare Dimokuraɗiyya” da kuma “A Dakatar da Yaƙi”, suna kira ga gwamnati da ta mutunta haƙƙokin jama'a da tsarin dimokuraɗiyya.

Rahotanni sun nuna cewa galibin zanga-zangar ta gudana cikin lumana, inda jami’an tsaro suka sanya ido domin tabbatar da zaman lafiya da tsaro a wuraren da aka gudanar da gangamin.

Masana harkokin siyasa na ganin cewa wannan gagarumin gangami na iya nuna yadda ake ƙara samun rabuwar kai a siyasar Amurka, tare da nuna damuwar al’umma kan batutuwan tsaro, tattalin arziƙi da kuma hulɗar kasashen duniya.

Ana sa ran cewa irin waɗannan gangami za su ci gaba a kwanaki masu zuwa yayin da ake ci gaba da muhawara kan manufofin gwamnati da makomar siyasar Amurka.

Comments

Popular posts from this blog

BREAKING: FG Approves 40% Pay Rise —Non-Academic Staff Left Out

Nigeria’s Ivory Towers in Ruins: An Investigative Look at the Dilapidated State of Nigerian Universities

BREAKING: US Finally Withdraws from WHO