TAKAICI YA ƘARU A ISRA’ILA: Dubban Jama’a Sun Fito Tituna Suna Neman A Rushe Gwamnatin Netanyahu, A Yi Zaɓen Gaggawa
Zanga-zanga ta ɓarke a manyan biranen ƙasar Isra'ila, musamman a biranen Ƙudus da Tel Aviv, inda dubban ‘yan ƙasa ke kira da a rushe gwamnatin Firayim Minista Benjamin Netanyahu tare da gudanar da zaɓen gaggawa.
Rahotannin da jaridar Zancen Yau247 ta samu, sun nuna cewa wannan shi ne karo na huɗu na zanga-zangar da ake yi a cikin ‘yan makonnin nan, bayan hare-haren sama da aka danganta da Iran da kuma harba makamai masu linzami daga ƙungiyar Hezbollah.
Masu zanga-zangar sun bayyana cewa ci gaba da yaƙin da gwamnati ke yi na iya jefa ƙasar cikin haɗari mai tsanani, suna masu zargin cewa an jefa su cikin rikicin da ba su so. Wasu daga cikin masu zanga-zangar sun riƙa rera taken cewa: “Mun manta yadda ake zama mutane.”
Rahotannin sun nuna cewa sama da kashi 75 cikin 100 na al’ummar ƙasar suna goyon bayan murabus ɗin Firayim Minista Netanyahu, tare da buƙatar a gudanar da sabon zaɓe domin bai wa jama’a damar zaɓar sabuwar shugabanci.
Wannan matsin lamba na jama’a ya ƙara tsananta ne a daidai lokacin da ake ci gaba da rikicin soji a yankin Gabas ta Tsakiya, wanda ya haɗa da hare-haren da ake kai wa juna tsakanin Isra’ila da maƙiyanta.
A gefe guda kuma, miliyoyin jama’a a ƙasar Amurka sun gudanar da zanga-zanga a ƙarƙashin taken “No Kings”, inda aka shirya sama da taruka 3,200 a jihohi 50 na ƙasar.
Masu zanga-zangar a Amurka na nuna rashin amincewa da shugabancin tsohon shugaban ƙasar Donald Trump da manufofinsa, lamarin da ya nuna yadda jama’a a ƙasashe daban-daban ke nuna damuwa kan shugabanninsu a wannan lokaci.
Comments
Post a Comment