Sarkin Fulani Ya Bayyana Dalilin Da Ya Sa Suka Mara Wa Gwamna Baya Shiga APC
Sarkin Fulanin Zamfara, Hon. Dr. Shehu Ahmed, ya bayyana cikakken goyon bayansa ga matakin da Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya ɗauka na komawa jam’iyyar APC, yana mai cewa wannan shawara ce da za ta kawo cigaba ga jihar.
Dr. Shehu Ahmed ya bayyana hakan ne yayin wata hira da manema labarai a dandalin taron karɓar Gwamna Lawal cikin jam’iyyar APC, inda ya jaddada cewa suna tare da gwamnan a wannan tafiya ta siyasa.
Ya ce sun amince da hukuncin da gwamnan ya ɗauka, domin sun yi imanin cewa yana da kyakkyawar manufa da kuma fata na alheri ga al’ummar jihar Zamfara.
A cewarsa, matakin da Gwamna Lawal ya ɗauka zai iya buɗe sabbin hanyoyi na bunƙasa tattalin arziƙi, samar da zaman lafiya, da kuma kawo ƙarshen hare-haren ‘yan bindiga da suka addabi jihar.
Hakazalika, Sarkin Fulanin ya yi kira ga al’ummar jihar Zamfara da su ci gaba da yi wa gwamnan addu’a, domin Allah Ya sanya wannan sauyi ya zama alheri ga jihar baki ɗaya.
Ya ƙara da cewa haɗin kai tsakanin shugabanni da al’umma shi ne ginshiƙin samun ci gaba mai ɗorewa da zaman lafiya a kowace al’umma.
Comments
Post a Comment