‘Mun Gaji da Ta’aziyya Kawai’ — CAN Ta Buƙaci Mataki Na Gaggawa Bayan Harin Ranar Lahadi a Jos

Kungiyar Kiristoci ta Najeriya, wato (CAN), ta yi kakkausar suka kan harin da aka kai a ranar Lahadi a jihar Filato, inda ta buƙaci gwamnati da jami’an tsaro su ɗauki matakan gaggawa domin kawo ƙarshen kashe-kashen da suka addabi yankin.

Harin da ya faru a unguwar Angwan Rukuba, ƙaramar hukumar Jos ta Arewa, ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama tare da jikkata wasu, lamarin da ya tayar da hankalin jama’a a faɗin ƙasar nan da ma ƙasashen waje.

CAN: ‘’Yan Najeriya Sun Gaji da Gafara Sa...’

A cikin wata sanarwa da shugaban CAN, Daniel Okoh, ya fitar, ya bayyana harin a matsayin abin takaici kuma wanda ba za a amince da shi ba.

Ya ce lokaci ya yi da gwamnati za ta wuce matakin yin ta’aziyya kawai, ta fara ɗaukar matakan da za su tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi.
Ya kara da cewa:

“’Yan Najeriya sun gaji da makoki, sun gaji da zntukan baki; abin da suke buƙata yanzu shi ne aiki.”

Ƙungiyar ta kuma buƙaci a gaggauta kama waɗanda suka aikata wannan ta’asa tare da gurfanar da su a gaban kuliya domin tabbatar da adalci.

Yadda Harin Ya Faru

Rahotanni sun nuna cewa ‘yan bindiga sun kai farmaki cikin dare a ranar Lahadi, suna harbin fararen hula ba ƙaƙƙautawa, lamarin da ya jefa al’ummar yankin cikin firgici. Wasu rahotanni sun ce maharan sun yi amfani da kayan sojoji na bogi domin yaudarar jama’a kafin su buɗe wuta.

An bayyana cewa ranar Lahadin, wadda a al’ada rana ce ta ibada da zaman lafiya, ta koma rana ta zubar da jini bayan da maza da mata da yara suka rasa rayukansu a harin.

Fushin Jama’a da Ƙarin Damuwa Kan Rashin Tsaro

Bayan harin, mazauna yankin sun gudanar da zanga-zanga domin nuna fushinsu, yayin da masu sharhi kan al’amuran tsaro suka bayyana cewa yawaitar hare-haren a yankin na nuna gazawar shugabanci da tsarin tsaro.

Masana sun jaddada cewa hare-haren da ake yawan kai wa a yankin na Arewa ta Tsakiya sun kara dagula matsalar tsaro a Najeriya, inda mutane da dama ke rayuwa cikin tsoro da rashin tabbas.

Comments

Popular posts from this blog

BREAKING: FG Approves 40% Pay Rise —Non-Academic Staff Left Out

Nigeria’s Ivory Towers in Ruins: An Investigative Look at the Dilapidated State of Nigerian Universities

BREAKING: US Finally Withdraws from WHO