Kwankwaso Ya Fice Daga NNPP, Yana Shirin Komawa ADC

Kano, Najeriya – Rahotannin da jaridar Zancen Yau247 ta samu a daren nan ya nuna yiwuwar jagoran ƙasa na (NNPP), Dr Rabiu Musa Kwankwaso, ya fice daga jam’iyyar NNPP kuma yana shirin shiga jam'iyyar (ADC). 

Wannan lamari na zuwa ne yayin da ake zargin cewa shi ma tsohon mataimakin gwamnan Kano, Nasiru Gawuna, na iya barin (APC) don shiga sabon dandali na siyasa.

A wani lokaci na rikicin siyasa, Mataimakin Gwamnan Kano, Aminu Abdussalam, ya miƙa takardun ajiye mukaminsa, inda aka bayyana hakan a matsayin mataki don tabbatar da zaman lafiya da cigaban mulki a jihar.

Kwankwaso na shirin haɗa ƙarfi da shugabannin adawa irin su Peter Obi da Atiku Abubakar, wanda hakan zai sake dagula lamarin siyasar Kano, musamman a masaukin Gwamna Abba Yusuf da jam’iyyar APC.

Masu sharhi a Kano sun bayyana cewa idan Kwankwaso ya shiga ADC, hakan zai canza yanayin zaben shugaban ƙasa na 2027, haka kuma zaɓen gwamna a jihar zai samu sabon salo idan Gawuna ma ya shiga ADC.

Comments

Popular posts from this blog

BREAKING: FG Approves 40% Pay Rise —Non-Academic Staff Left Out

Nigeria’s Ivory Towers in Ruins: An Investigative Look at the Dilapidated State of Nigerian Universities

BREAKING: US Finally Withdraws from WHO