Kwana Huɗu Babu Barci: Al’ummar Ɗan Sadau A Zamfara Sun Kare Kansu Daga Hare-haren ‘Yan Bindiga

Maru, Jihar Zamfara — Al’ummar garin Ɗan Sadau da ke ƙaramar hukumar Maru a Jihar Zamfara sun ɗauki matakin kare kansu daga hare-haren ‘yan bindiga, inda suka shafe kwanaki huɗu ba tare da barci ba suna tsaron yankinsu.

Rahotannin da jaridar Zancen Yau247 ta samu daga yankin sun nuna cewa mazauna garin sun shirya tsaron dare da rana domin hana ‘yan bindiga sake kai farmaki, lamarin da ya sa aka samu zaman ɗar-ɗar a yankin cikin kwanakin nan.

Majiyoyi daga cikin al’ummar sun bayyana wa jaridar Zancen Yau247 cewa duk da ƙoƙarin da suke yi, har yanzu ba su samu isasshen tallafi daga gwamnati ba, wanda suka ce hakan na ƙara jefa su cikin haɗari.

Wasu daga cikin mazauna yankin sun shaida a cikin wani fefen bidiyo da suka ɗauka a ɗaya daga cikin ranakun da suka yi artabi da wasu ɓarayin dajin da suka cikin garin, suka kuma yaɗa, cewa sun shiga cikin mawuyacin hali sakamakon hare-haren da ake yawan kai musu, wanda ya tilasta musu ɗaukar matakin kare rayukansu da dukiyoyinsu da kansu.

Al’ummar Ɗan Sadau sun yi kira ga gwamnatin Jihar Zamfara da gwamnatin tarayya da su gaggauta tura jami’an tsaro zuwa yankin domin kawo ƙarshen matsalar tsaro da ke addabar su.

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, hukumomin tsaro da gwamnatin jihar ba su fitar da wata sanarwa a hukumance kan halin da ake ciki a garin na Ɗan Sadau ba.

Comments

Popular posts from this blog

BREAKING: FG Approves 40% Pay Rise —Non-Academic Staff Left Out

Nigeria’s Ivory Towers in Ruins: An Investigative Look at the Dilapidated State of Nigerian Universities

BREAKING: US Finally Withdraws from WHO