Gwamnatin Jihar Zamfara Za Ta Ɗauki Malaman Makaranta 2,000


Gwamnatin jihar Zamfara ta sanar da shirin ta na ɗaukar sabbin malaman makaranta har guda 2,000 domin cike giɓin da ake da shi a makarantu a faɗin jihar.

Kwamishinan Kasafin Kuɗi da Ilimi na jihar, Abdulmalik Abubakar Gajam, ne ya bayyana hakan bayan wata muhimmiyar ganawa da kwamitin da aka kafa domin gudanar da aikin ɗaukar malaman.

A cewarsa, ganawar ta mayar da hankali ne kan tabbatar da cewa tsarin ɗaukar aikin ya kasance bisa gaskiya, da cancanta, kuma cikin ingantaccen tsari, domin tabbatar da cewa an kawo ƙwararrun malamai masu jajircewa cikin ajujuwa.

Ya ƙara da cewa wannan shiri wani muhimmin mataki domin Inganta ingancin ilimi a makarantu, da cike giɓin malamai da ake fuskanta

Kwamishinan ya jaddada cewa gwamnatin jihar na da niyyar zuba jari a fannin ilimi da bunƙasa jarin ɗan Adam, domin samar da ingantacciyar garkuwa ga cigaban al’umma.

“Mun kuduri aniyar gina tubali mai ƙarfi na ilmantarwa ta hanyar samar da malamai nagari da kuma ƙarfafa matasa domin su zama ginshiƙan ci gaban al’umma,” in ji shi.

Daga ƙarshe, Kwamishina Gajam ya tabbatar cewa gwamnati za ta ci gaba da aiki tare da masu ruwa da tsaki domin tabbatar da nasarar shirin, tare da tabbatar da cewa an gudanar da dukkan matakai cikin adalci da gaskiya.

Comments

Popular posts from this blog

BREAKING: FG Approves 40% Pay Rise —Non-Academic Staff Left Out

Nigeria’s Ivory Towers in Ruins: An Investigative Look at the Dilapidated State of Nigerian Universities

BREAKING: US Finally Withdraws from WHO