INEC Ta Sake Fitar da Sabon Jadawalin Zaben 2027 Bayan Dokar Zabe ta 2026 Ta Kama Aiki
A sanarwar da hukumar ta fitar daga shelkwatar ta a Abuja, INEC ta bayyana cewa sabunta jadawalin ya zama dole ne saboda canje-canje da sabuwar dokar zaben ta 2026 ta kawo, wanda ya shafi lokutan gudanar da zabuka da harkokin da suka gabace su.
Sabon jadawalin ya nuna cewa zaben shugaban kasa da na majalisar tarayya za a gudanar da su a Asabar, 16 ga Janairu 2027, yayin da zaben gwamna da na majalisun dokoki na jihohi za su gudana a Asabar, 6 ga Fabrairu 2027.
📅 Sabbin Ranakun Zabe
- Shugaban Kasa & Majalisar Tarayya: Asabar, 16 Janairu 2027
- Gwamnoni & Majalisun Dokoki na Jihohi: Asabar, 6 Fabrairu 2027
🗓️ Muhimman Ranaku
Zaben Fidda Gwanin Jam’iyyun Siyasa
- Fara: 23 Afrilu 2026
- Kammala: 30 Mayu 2026
Wannan ya ba jam’iyyun siyasa sama da wata guda domin gudanar da dukkan zaben fidda gwani na mukamai daban-daban.
Kamfen na Siyasa
- Kamfen din shugaban kasa da na majalisar tarayya zai fara a 19 Agusta 2026, kamar yadda sabuwar dokar ta tanada.
- Sauran kamfen-kan za su bi jerin lokacin da aka kayyade a jadawalin.
Dalilin Sauya Jadawalin
INEC ta bayyana cewa Dokar Zabe ta 2026 ta kawo sauye-sauye da suka shafi:
- Tsarin zaben fidda gwani
- Tsawon lokacin kamfen
- Ranakun mika jerin sunayen ‘yan takara
- Da sauran lokutan gudanar da manyan zabe
Saboda haka dole ne a daidaita sabbin jadawalan da abinda dokar ta tanada domin bada isasshen lokaci ga jam’iyyun siyasa, ‘yan takara, da sauran masu ruwa da tsaki.
Hukumar ta INEC ta jaddada cewa tana da cikakken shiri da niyyar gudanar da zabe mai inganci, gaskiya da sahihanci. INEC ta kuma yi kira ga jam’iyyun siyasa da su bi jadawalin yadda ya kamata domin kauce wa matsalolin doka da rikice-rikice a gaba.
Comments
Post a Comment