Amurka Na Son Kai Hari Kan Kasashen Musulmi Lokacin Azumi’ — Inji Ilhan Omar
Washington, DC — Ƙaruwar zargi kan manufofin tsaro na Amurka ya ƙara ɗaukar hankali bayan da wakilar majalisar dokoki ta Amurka, , ta yi ikirarin cewa Amurka tana kai hare-hare kan ƙasashen Musulmi musamman a watan Ramadan “saboda wadanda suke bautawa.”
A wata wallafa da ta yi a dandalin X, Omar ta zargi gwamnatin Amurka da rainin addinin Musulunci wajen tsara lokutan hare-haren soji, inda ta ce an kai hare-hare a Iraq cikin lokacin Azumi a baya, sannan yanzu ana barazanar kai hari kan Iran ma a irin wannan lokacin mai tsarki.
Ta ce hakan na nuna rashin girmama al’adun Musulmi, musamman ganin cewa Ramadan wata ce ta ibada, zaman lafiya da nutsuwa.
Takaddama Tsakaninta da Trump
Zargin Omar ya zo ne kwanaki kaɗan bayan takaddama tsakaninta da tsohon shugaban Amurka, , wanda a jawabin State of the Union ya kira ta da “mahaukaciya” tare da cewa ita da Rashida Tlaib “ya kamata a tura su inda suka fito.”
Maganganun Trump sun jawo cece-kuce a Amurka, inda ‘yan jam’iyyar Democrat da kungiyoyin kare haƙƙin bil’adama suka yi Allah-wadai da su a matsayin tsattsauran ra’ayi da wariyar kabilanci.
Omar Ta Ci gaba da Suƙar Siyasar Waje ta Amurka
Omar, wadda ta dade tana suƙar tsoma bakin Amurka a Gabas ta Tsakiya, ta ce ana yawan shirya hare-haren da ke haddasa mutuwar fararen hula ba tare da la’akari da ranakun ibada ko darajar al’adun yankin ba.
Ta kuma nuna damuwa kan yiwuwar sabon tashin hankali tsakanin Amurka da Iran, a daidai lokacin da ake rikice-rikice kan batun makamashin nukiliya da tsaro a yankin.
Masu Suka Sun Ce Lokutan Hare-Haren Ba Sa La’akari da Ramadan
Masu nazarin manufofin tsaro da dama sun sha sukar ginin tsare-tsare na Amurka wajen kai hare-hare a Afghanistan, Yemen, Somalia da sauran kasashen Musulmi, musamman idan hakan ya yi daidai da lokutan bukukuwan addini.
Sai dai hukumomin tsaro na Amurka kan ce dalilai na tsaro ne kawai suke amfani da su, ba kalandar addini ba.
Comments
Post a Comment