APC Ta Ce Katin Bello Turji Na APC Na Boge Ne
Jam’iyyar APC reshen jihar Zamfara ta fito karara ta musanta rahotannin da ke yawo a kafafen sada zumunta da ke nuna cewa fitaccen jagoran ‘yan bindiga, Bello Turji, mamba ne na jam’iyyar.
A wata sanarwa da jam’iyyar ta fitar, ta bayyana cewa katin membobinsu da ake nunawa a matsayin na Bello Turji ƙirƙirarre ne kuma an shirya shi ne da gangan domin bata sunan jam’iyyar a idon al’umma.
Jam’iyyar APC ta jaddada cewa ba ta da wata alaƙa da Bello Turji ko duk wani mutum da ke da hannu a ayyukan ta’addanci, fashi da makami ko kashe-kashe, tana mai cewa jam’iyyar ba za ta taba karɓar mutum mai laifi a cikinta ba.
Sanarwar ta ce:
“Jam’iyyar APC jam’iyya ce mai bin doka da oda, kuma ba za ta lamunci a jingina sunanta da ‘yan bindiga ko masu tayar da hankali ba. Katin da ke yawo a kafafen sada zumunta karya ce tsagwaron gaske.”
Jam’iyyar ta kuma yi kira ga hukumar tsaro da jami’an bincike da su gaggauta bincikar inda katin ya fito tare da daukar matakin doka kan duk wanda aka samu da hannu wajen ƙirƙirarsa da yada shi.
Haka zalika, APC ta bukaci ‘yan Najeriya da su yi watsi da labarin, tare da gujewa yada jita-jita da ka iya haddasa rikici ko bata sunan jam’iyyun siyasa.
Rahoton ya zo ne a daidai lokacin da ake ci gaba da ƙoƙarin gwamnatin tarayya da na jihohi wajen murkushe ayyukan ‘yan bindiga a arewa maso yammacin Najeriya, musamman a jihar Zamfara da ke fama da matsalar tsaro.
Comments
Post a Comment