An Cafke Wasu Shugabannin Miyett-Allah Bisa Zargin Garkuwa da Mutane
Ilorin, Jihar Kwara — Jami’an tsaro a Jihar Kwara sun cafke shugabannin ƙungiyar Miyetti Allah ta jihar, ciki har da Shugabanta, Idris Abubakar, bisa zargin hannu a sace-sacen mutane da kuma ɗaukar nauyin ƙungiyoyin ‘yan bindiga a wasu sassan jihar.
Rahotannin da jaridar ZANCEN YAU24 ta samu sun bayyana cewa an kama su ne bayan bayanan sirri da bincike mai zurfi da hukumomin tsaro suka gudanar, wanda ya danganta wasu mambobin ƙungiyar da hare-hare, garkuwa da mutane, da kuma taimaka wa ƙungiyoyin ‘yan bindiga da ke addabar al’ummomi a Kwara da kewaye.
Wata majiya ta tsaro ta bayyana wa jaridar ZANCEN YAU24 cewa kamun ya zo ne a wani sabon mataki na gwamnati na murƙushe ayyukan ta’addanci da rashin tsaro da ke ƙaruwa a jihar. Ana sa ran za a gurfanar da waɗanda aka kama a gaban kotu bayan kammala bincike.
Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, shugabancin Miyetti Allah na ƙasa bai fitar da wata sanarwa ba kan lamarin.
Comments
Post a Comment