Yanzu-Yanzu: Mummunan Harin Da Iran Ta Kai Isra'ila Yayi Sanadiyar Mutuwar Mutum 12

Aƙalla mutane 12 ne suka mutu, yayin da daruruwan wasu suka jikkata, bayan Iran ta ƙaddamar da sabon hari na manyan makaman masu linzami zuwa sassa daban-daban na ƙasar Isra'ila, lamarin da ya kara dagula halin rashin zaman lafiya a Yankin Gabas ta Tsakiya.

Rahotanni sun tabbatar da cewa garin Beit Shemesh, kusa da birnin Kudus, shi ne ya fi shan lamarin lokacin da wani babban makami ya faɗa kai-tsaye cikin unguwar jama’a, ya tarwatsa gidaje, ya rushe wani wurin ajiyar bamabamai, tare da haddasa asarar rayuka da dama.

Hukumomin agajin gaggawa na Kasar Israila sun ce aƙalla mutane tara (9) ne suka mutu a harin Beit Shemesh kaɗai, inda ginin da makaman suka buga ya rushe gaba ɗaya, wasu mazauna har yanzu ana zaton sun makale a ƙarƙashin burabuzan ginin.

An kuma samu ragargazar gini da jikkata a wasu sassan tsakiyar kasar, ciki har da yankin Tel Aviv, inda aka tabbatar da mutuwar wasu mata biyu yayin da suke kokarin shiga mafaka ko kuma sakamakon fashewar makami.

An ce an yi ta Jin karar agajin gaggawa Inda suka dauki lokaci suna tashi a birane da dama yayin da garkuwar kariya ta sama ta Kasar Israila ke kokarin tarwatsa makaman. Duk da haka, an tabbatar da cewa wasu makaman sun tsallake garkuwan suka bugi yankunan jama’a.

Agaji da Ceto Sun Ci Gaba
Kungiyoyin agaji kamar Magen David Adom da United Hatzalah sun shiga aikin ceto cikin dare, inda ake fitinar neman wadanda suka makale a karkashin duwatsu da turɓaya. Motocin asibiti da jiragen sama masu saukar ungulu na ta kai-komo da masu jikkata zuwa cibiyoyin lafiya.

Sabon harin ya biyo bayan rundunar sojin Iran da ta sha alwashin ramuwa bayan rahotannin cewa harin hadin guiwar Amurka da Israila ya kashe Ayatollah Ali Khamenei da manyan hafsoshin Iran. Tehran ta bayyana cewa wannan martani ne kan abin da ta kira barazana ga wanzuwarta.

HalIN Tashin Hankali Ya Karu
Al’umma a Isra’ila na cikin tashin hankali, yayin da shugabanin kasar ke kira ga ɗorewar martani ga Iran. A gefe guda, Iran na cikin kwanakin alhinin kasa, inda jami’an gwamnati ke cewa rikicin zai “koma matakin da ba a taba gani ba”.

Comments

Popular posts from this blog

BREAKING: FG Approves 40% Pay Rise —Non-Academic Staff Left Out

Nigeria’s Ivory Towers in Ruins: An Investigative Look at the Dilapidated State of Nigerian Universities

BREAKING: US Finally Withdraws from WHO