Yadda Rikicin Gabas Ta Tsakiya Ke Neman Hana Umarar Bana
Akwai tsananin damuwa da rashin tabbas a tsakanin ɗaruruwan ‘yan Najeriya da ke shirye-shiryen gudanar da Umarah a ƙasar Saudi Arabia, sakamakon yadda rikicin da ya kunno kai tsakanin Iran da Amurka ke ci gaba da shafar zirga-zirgar jiragen sama a yankin Gabas ta Tsakiya.
Rahotanni sun tabbatar da cewa jiragen sama da dama sun dakatar da zirga-zirga ko kuma sun sallama fasinjoji ba tare da tashi ba, lamarin da ya bar wasu maniyyata daga Najeriya cikin kunci da rashin tabbas a filayen jiragen sama.
Jiragen Daga Najeriya Sun Gamu Da Cikas
Yawancin maniyyatan Umarah daga Najeriya na tafiya ne ta manyan filayen jiragen ƙasashen Gabas Ta Tsakiya kamar Doha, Dubai, Abu Dhabi da Jeddah. Amma sabanin haka:
An rufe wasu sassan sararin samaniyar yankin saboda tsaro.
Manyan kamfanonin jirage irin su Qatar Airways, Emirates da Turkish Airlines sun dakatar da ko jinkirta tashi.
Wasu ‘yan Najeriya sun kai filin jirgi, aka karɓi kayan su, amma daga ƙarshe jiragen suka soke tafiya. Wannan ya haifar da halin kaka-nika-yi a tsakanin kamfanonin shirya tafiya waɗanda ke fuskantar matsin lamba wajen sake tsara tikiti, neman madadin hanya da kare mutuncin kamfanoninsu.
Gwamnati Ta Yi Gargadi
Hukumar kula da filayen jiragen sama ta Najeriya (FAAN) ta bayyana cewa:
Rikicin Iran da Amurka/Isra’ila ya haifar da takaita zirga-zirga a ƙasashen Gabas.
Ta bukaci maniyyata su dinga tantance jadawalin jiragen su a kai-a-kai.
Ta yi kira ga ‘yan ƙasa da su guji yin balaguro da ba dole ba yayin da tashin hankali ke ci gaba.
Halin Da Maniyyatan Ke Ciki
Wasu maniyyata da tuni suka biya kudaden su na tafiya, da dama daga cikin su suna cikin:
Fargabar rasa lokacin Umarah, musamman ma waɗanda aka yi wa jadawalin tafiya a lokuta na musamman.
Damuwa kan dawo da kuɗi, musamman idan jiragen sun soke tafiya kwatsam.
Rashin tabbas kan ko za a ga sauƙin wannan rikici a mako mai zuwa ko kuma a sami tsawaitawa.
Ba ‘yan Najeriya kaɗai suka shiga damuwa ba;
Kasashen Asiya kamar Indonesia da Malaysia ma sun bayyana cewa dubban maniyyatansu na cikin ruɗani da rikice-rikicen tafiya saboda dakatar da jirage daga Gabas Ta Tsakiya.
Masana harkokin jiragen sama sun ce rikicin na iya haifar da asarar sama da dala biliyan ɗaya ga kamfanonin jirage idan halin bai lafa ba.
Rikicin Iran da Amurka/Isra'ila ya zama babban kalubale ga maniyyatan Umarah na bana, musamman daga Najeriya. Yayin da halin tsaro a Gabas ta Tsakiya ke ci gaba da tangal-tangal, ana sa ran za a iya samun karin jinkiri ko sokewar jirage. Maniyyata za su ci gaba da jiran sanin makomar tafiyarsu.
Comments
Post a Comment