Kasuwancin Makamai Ba Bisa Ka’ida Ba Na Rura Wutar Rashin Tsaro a Yammacin Afirka – Rahoto

Wani sabon rahoto da Defence Watch Africa ta wallafa ya bayyana yadda yawaitar safarar makamai ba bisa ka’ida ba ke ci gaba da ƙara muni ga matsalolin tsaro da ke addabar ƙasashen Yammacin Afirka.

Rahoton ya nuna cewa duk da ana yawan danganta matsalolin yankin da ta’addanci, garkuwa da mutane, tada ƙayar baya da kuma ayyukan ƙungiyoyin masu aikata laifuka, akwai wani muhimmin abin da ke bai wa waɗannan matsaloli ƙarfi, wato yaɗuwar ƙananan makamai da makaman yaƙi ba tare da izini ba.

A cewar rahoton, daga dazukan kudancin Najeriya zuwa yankunan Sahel da suka haɗa da Mali, Burkina Faso da Nijar, makamai na ci gaba da shiga hannun masu aikata laifuka ta hanyoyi daban-daban, lamarin da ke ƙara ta’azzara rashin tsaro a yankin.

Masana tsaro sun bayyana cewa yawaitar waɗannan makamai na bai wa ƙungiyoyin ’yan ta’adda, masu garkuwa da mutane da sauran masu aikata laifuka damar gudanar da hare-hare cikin sauƙi, tare da ƙara jefa al’umma cikin fargaba da rashin zaman lafiya.

Rahoton ya kuma yi gargadin cewa idan ba a ɗauki tsauraran matakai wajen dakile hanyoyin da ake safarar makamai ba, ƙasashen Yammacin Afirka za su ci gaba da fuskantar manyan ƙalubalen tsaro da ke barazana ga rayuka da dukiyoyin jama’a.

Defence Watch Africa ta buƙaci gwamnatocin yankin da hukumomin tsaro su ƙara haɗa kai wajen gano hanyoyin da ake shigar da makamai ba bisa ƙa’ida ba, tare da ƙarfafa sa ido kan iyakoki domin rage yawaitar makaman da ke haddasa rikice-rikice a faɗin yankin.

Comments

Popular posts from this blog

BREAKING: FG Approves 40% Pay Rise —Non-Academic Staff Left Out

Nigeria’s Ivory Towers in Ruins: An Investigative Look at the Dilapidated State of Nigerian Universities

BREAKING: US Finally Withdraws from WHO